Shugaban hadakar jam'iyyun adawar kasar NASA, Musalia Mudavadi ya ce, sakamakon zaben dake cikin babbar na'urar adana bayanai ta hukumar zaben kasar, IEBC, ya nuna cewa, Odinga ne ya yi nasara a zaben da yawan kuri'u miliyan 8.4, inda ya dara Kenyatta mai kuri'un miliyan 7.75.
Ya ce wata majiya ce daga hukumar zaben kasar ta sheda musu sakamakon zaben a daidai lokacin da ake samun bayanai dake cin karo da juna, lamarin da aka iya jefa kasar cikin tashin hankali sai dai NASA ta ce wannan ba shi ne burinta ba. (Ahmad Fagam)