in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakon da Obama ya aike a shafin sada zumunta game da tashin hankalin Charlottesville ya shiga tarihi
2017-08-17 10:45:25 cri
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, sama da mutane miliyan uku dake bibbiyar shafin sada zumunta na Twitter ne suka nuna amincewa da martanin da tsoshon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya mayar game da tashin hankalin da ya barke a karshen makon da ya gabata a garin Charlottesville dake jihar Virginia na kasar ta Amurkar, abin da ke nuna cewa, sakon na Obama ya karya kambun bajinta sakonnin da suka fi farin jini da aka wallafa a shafin na twitter.

Sakon na Obama dai ya fara ne da cewa, " Babu wanda aka haifa da kin jinin wani, saboda launin fatarsa ko asalinsa ko kuma addininsa." sakon tsohon shugaban Amurkar da ya wallafa a ranar Asabar da dare, ya tsamo nashi ne daga littafin tarihin tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu, marigayi Nelson Mandela mai suna "Long Walk to Freedom" a Turance wato "gwagwarmayar kwatar 'yanci".

Haka kuma a gefen sakon da ya wallafa, Obama ya kuma wallafa wasu hotunansa da ya dauka a cibiyar renon yara a Bethesda dake jihar Maryland a shekarar 2011, yana yiwa wasu kananan yara daga rukunin al'umma daban-daban murmushi, hotunan da tsohon mai daukar hoton fadar Whites House Pete Souza ya dauka.

Sako na baya-bayan da ya yi farin jini, shi ne wanda fitacciyar mawakiyar nan Ariana Grane ta wallafa, game da mummunan harin nan da aka kai a gidan rawarta dake Ingila, inda masu bibiyar shafin sada zumunta na twitter suka kaunaci sakon sau miliyan 2.7

Sakon da Obaman ya wallafa a ranar 12 ga watan Agusta wanda shi ne na farko cikin makonni uku, na zuwa ne bayan wani mummunan tashin hankali mai nasaba da masu fifita fararen fata zalla ya barke a kwalejin Charlottesville mai dadadden tarihi a karshen mako. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China