in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta tabbatar da samun takardar ficewa daga yarjejeniyar Paris da Amurka ta aike mata
2017-08-05 14:01:43 cri
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya samu takardar ficewar Amurka daga yarjejeniyar Paris da zaunannen wakilin kasar dake majalisar ya gabatar.

Wata sanarwar da kakakin babban magatakardan Stephane Dujarric ya fitar ga manema labarai a jiya, ta ce wakilin Amurka ya ce ya kamata yanzu kasar ta fice bisa ka'idojin yarjejeniyar.

Sai dai Mr. Dujarric ya ce, babban magatakardan ya ce, zai yi maraba da dawowar Amurka cikin yarjejeniyar ta Paris a kowanne lokaci.

Haka zalika, ya sake jaddada matsayin da babban magatakardan MDD ya dauka bayan Amurka ta sanar da ficewarta daga yarjejeniyar a ranar 1 ga watan Yunin bana, inda Antonio Guterres ya ce, ficewar kasar daga yarjejeniyar Paris abu ne da ya bata ran al'ummomin kasa da kasa, sabo da matsalolin da za ta haifar ga ayyukan rage fitar da iska mai gurbata muhalli, da kuma kiyaye tsaron kasa da kasa.

Bugu da kari, ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar kalubale da dama ta fuskar sauyin yanayi, yana mai cewa zai fi kyau idan Amurka za ta iya ci gaba da jagorantar ayyukan kare muhalli.

Ya ce a matsayinsa na babban magatakardan MDD, yana sa ran Amurka za ta yi hadin gwiwa da kasashe wajen kyautata muhallin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China