in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya bukaci wakilin cinikayyar Amurka ya bincike zargin da ake yi wa kasar Sin game da kare mallakar fasaha
2017-08-15 09:27:36 cri

A jiya Litinin ne, shugaba Trump na kasar Amurka ya umarci wakilin harkokin cinikayyar kasar (USTR) Robert Lighthizer da ya bincike zargin da ake yi wa kasar Sin game da ayyukan ta na kare mallakar fasaha, duk da fargabar da hakan ka iya yi wa dangantakar cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Trump ya ba wannan umarni ne a fadar White House, gabannin sanya hannu kan wata doka da ta baiwa wakilin na Amurkar iznin duba wannan batu.

Sai dai ba a san ko Mr. Lighthizer zai gudanar da bincike a hukumance game da zargin da ake yi wa kasar Sin kan wannan batu ba. Yanzu haka wannan mataki ya haifar da damuwa game da rikicin cinikayya tsakanin manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta nazarci ci gaban da kasar ta Sin a fannin kare mallakar fasaha da idon basira, kana ta warware bambance-bambancen dake tsakaninsu da kasar Sin ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China