in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta ce a shirye take ta shiga tattaunawa da Amurka
2017-08-07 10:16:01 cri
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce a shirye Moscow take ta shiga tattaunawa da Washington, matukar Washington din ta jingine matakinta na yin fito na fito da Moscow.

Sergei Lavrov ya bayyana haka ne jiya a babban birnin kasar Philippine, lokacin da ya gana da takwaransa na Amurka Rex Tillerson a wani bangare na jerin tarukan ministocin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asia wato ASEAN.

Bangarorin biyu sun tattauna kan yadda Rasha za ta tunkari takukuman da Amurka ta kakaba mata.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta hanun kamfanin dillancin labaran Tass, Sergei Lavrov ya ce babu yadda za a yi a ce ba a mai da martini ga takunkuman na Amurka ba, ciki har da kwace kadarorin Rashar da ta yi ba bisa ka'ida ba tun cikin watan Disamban bara.

Sai dai ya ce, duk da haka, a shirye Moscow take ta tattauna da Washington idan ta jingine matakanta na fito na fito. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China