A wata sanarwar da fadar White House ta fitar, Trump ya bayyana cewa duk da cewa matakai ne da aka dauka domin ladaftarwa kan kasashen Iran da DPRK kuma matakin yana son bayyanawa Rasha karara cewa, Amurka ba za ta taba lamuntar duk wani yunkuri na yin shishshigi cikin harkokinta na siyasa ba, sai dai ya kalubalanci dokar da cewa ta kunshi wasu batutuwa da suka saba tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar, kuma a cewarsa wannan babban kuskure ne.
A farkon wannan wata ne dai kudurin dokar ya samu amincewar majalisar dokokin kasar ta Amurka, duk kuwa da bukatar da gwamnatin Trump ta nuna na neman majalisar ta yi sauye sauye kan dokar sakamakon alakar dake tsakanin Amurkar da Rasha. (Ahmad Fagam)