Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "dangantakar dake tsakaninmu da Rasha tana cikin hadari a ko da yaushe kuma dokar tana da matukar hadari. Za ka iya godewa majalisar, kuma mutanen dai su ne wadanda ba sa iya ba mu tsarin kiwon lafiya".
Tsokacin na mista Trump na zuwa ne kwana guda bayan da majalisar dokokin Amurkar ta amince da dokar kakabawa Rasha da Iran da Koriya ta arewa takunkumi, sai dai ya bayyana dokar da cewa tana da matukar kura kurai.
Sabanin dokokin da ake da su a baya, sabbin dokokin na Amurka sun baiwa majalsar ikon takawa Trump birki daga dagewa Rashar duk wani takunkumi.
Wannan kuduri dai ya samu gagarumin amincewa daga 'yan majalisar dokokin na Amurka tun a farkon wannan wata, duk da rokon da gwamnatin Trump ta yi, na neman su amincewar fadar ta White House wajen sassauta dokar saboda dangantakar dake tsakanin Amurkar da Rasha.
A martanin da ta mayar dangane da sabuwar dokar da majalsar ta zartar na kakaba mata takunkumi, tuni Moscow ta amince da zaftare adadin jami'an diplomasiyyar Amurka 755 dake kasar Rashar. (Ahmad Fagam)