Ministan cinikayya na kasar Sin Zhong Shan, kana shugaban taron ministocin cinikayyar kasashen na BRICS karo na bakwai, wadanda suka hada da kasashen Brazil, Rasha, Indiya da Sin da kuma Afirka ta kudu, shi ne ya bayyana hakan a jawabinsa na bude taron na kwanaki biyu a jiya Talata.
Zhong ya kuma yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu kana su bullo da sabbin matakai, sakamakon rashin tabbas da farfadowar tattalin arzikin duniya ke fuskanta.
Tun lokacin da aka kafa kungiyar ta BRICS a shekarar 2006, kasashen na BRICS suka bullo da sabbin matakan cin moriyar juna a tsakanin kasashe masu tasowa. Kuma ya zuwa yanzu, Kasashen BRICS sun taka muhimmiyar rawa a sha'anin shugabanci da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya. (Ibrahim Yaya)