in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen kungiyar BRICS sun sha alwashin yaki da sanyawa kasuwanni shinge
2017-08-02 21:07:30 cri

Ministocin kasuwanci na kasashe mambobin kungiyar BRICS, sun amince da kudurin yakar yi wa kasuwanni shinge, suna masu fatan kasashen kungiyar za su yi hadin gwiwa, wajen inganta cudanyar hada hada tsakanin su. Ministocin sun cimma wannan matsaya ne a taronsu na yau wanda ya gudana a birnin Shanghai.

Cikin wata sanarawar bayan taron da wakilan kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta Kudu, wadanda kuma mambobi ne na kungiyar cinikayya ta duniya WTO suka fitar, sun kuduri aniyar taka karin rawar gani, wajen bunkasa tattalin arzikin duniya. Don haka suka bukaci sauran kasashen kungiyar ta WTO, da su ma su rungumi wannan kuduri na baiwa kasuwa damar yin halinta.

Kaza lika sun mika gayyata ga karin kasashen duniya, kan su shiga kungiyar ta WTO don a dama da su. A hannu guda sun bukaci sassan hukumomin da wannan batu ya shafa, da su kara himmantuwa wajen karbar kasashe masu karancin wadata cikin kungiyar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China