in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude reshen sabon bankin raya kasa na kasashen BRICS a Afirka ta kudu, in ji shugaban bankin
2017-08-10 20:34:07 cri
Shugaban sabon bankin raya kasa na kasashen BRICS K.V.Kamath ya bayyana a jiya Laraba a birnin Shanghai cewa, za a bude reshen bankin na farko a kasar Afirka ta kudu a ranar 17 ga wata.

Ya ce, bisa ga shirin bankin, nan da shekaru biyar masu zuwa, za a ware kimanin kashi biyu daga cikin uku na rancen kudaden da bankin ke samarwa ga bangaren raya muhimman ababen more rayuwa da za su taimaka ga samun dauwamammen ci gaba.

Ya kara da cewa, reshen bankin da za a bude a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu a mako mai zuwa shi ne reshe na farko da bankin ya bude, wanda kuma zai taimaka wa bankin wajen aiwatar da shirye-shiryensa a nahiyar Afirka, ta yadda zai kasance kofar bankin na shiga nahiyar Afirka.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China