Ministocin sun dauki wannan mataki ne jiya, bayan kammala taronsu na shekara da ya gudana a Shanghai na kasar Sin.
Wata sanarwa da suka fitar bayan taron ta ce, dukkan kasashen kungiyar da suka hada da Brazil da Rasha da Indiya da Sin da Afrika ta kudu mambobi ne na Hukumar WTO mai kula da harkokin cinikayya ta duniya, wadanda kuma ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.
Ministocin sun kuma yi kira da sauran kasashe su bi sahunsu wajen yaki da shingayen cinikayya, suna masu karfafa musu gwiwar shiga a dama da su cikin hukumar WTO, inda kuma suka bukaci hukumar ta kara mai da hankali kan kasashe masu tasowa.
Kasar Sin dake rike da shugabancin kungiyar BRICS a bana, za ta karbi bakuncin babban taron kungiyar karo na 9 cikin watan Satumba mai zuwa a Xiamen na lardin Fujian. (Fa'iza Mustapha)