Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Talata, kakakin rundunar sojin kasar Tamer el Refai, ya ce sojoji sun kashe wasu muggan 'yan tada kayar baya yayin wani samame da su ka kai ta sama da kasa a biranen dake arewacin lardin Sinai da suka hada da Arish da Rafah da Sheikh Zuweid.
Har ila yau, ya ce an kuma damke wasu guda 5 yayin samamen.
Tun bayan hambarar da mulkin tsohon shugaba Mohammed Morsi da sojoji suka yi a shekarar 2013, Masar ke fama da matsalar rashin tsaro, galibi a lardin Sinai, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan jami'an tsaro (Fa'iza Mustapha)