Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta bayyana cewa, 'yan sanda sun afkawa sansanin da Muslim Brotherhood suke horas da mayakansu masu alaka da Hasm, dake Fayoum wanda ke da tazarar kilomita 100 a kudu maso yammacin birnin Cairo.
'Yan sandan sun yi dirar mikiya a sansanin ne, bayan samun wasu muhimman bayanai dake nuna cewa kungiyar tana shirin kaddamar da hare haren ta'addanci a kasar.
Sanarwar ta kara da cewa, an hallaka 'yan ta'addan ne bayan da suka budewa 'yan sanda wuta suna kokarin afka musu.
A yan kwanakin nan 'yan sanda sun hallaka mayaka 22 a lardin Giza dake kusa da Cairo a Suez Canal dake birnin Ismailia. An yi amanna cewa kungiyar Hasm tana zaune ne a birnin Cairo, kuma tana da alaka da kungiyar Muslim Brotherhood, da kuma kungiya mai fafutukar kafa daular musulunci ta IS dake da sansaninta a zirin Sinai.