in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asibitoci a Nijeriya sun inganta matakan sa ido kan cutar zazzabin lassa
2017-08-10 09:28:25 cri
Ana inganta matakan sa ido da na bibiyyar harkoki a asibitin koyarwa na Lagos, inda aka samu mutuwar mutane biyu da kuma wasu mutane dari da aka kebe saboda cutar zazzabin lassa.

Yayin da marasa lafiya ke ganin likitoci da masu aikin jinya a sashen kula da bukatun gaggawa, an ga masu shara sanye da makarin fuska da safar hannu suna ta tsaftace dakuna da harabar asibitin.

Reshen kungiyar likitoci ta jihar Lagos ta kira da wayar da kan al'umma, tana mai bukatar su kula da tsaftar jiki da na muhalli don kare ci gaba da yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China