in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bada rahoton barkewar cutar kyanda a wata jiha a Najeriya
2017-08-10 09:36:47 cri
Hukumomin lafiya a Najeriya sun bada rahoton barkewar cutar kyanda a kananan hukumomi 10 na jihar Taraba dake arewacin kasar.

Innocent Vakkai, shi ne kwamishinan lafiya na jihar, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga 'yan jaridu a garin Jalingo, babban birnin jihar, ya ce tuni gwamnatin jihar ta fara aikin gangamin dakile yaduwar cutar, inda ta horar da jami'an lafiya masu yawa, kuma ta tura su sassan jihar domin dakile cutar.

Vakkai ya shawarci iyaye da su tabbatar sun mika 'ya'yansu domin ba su rigakafin cutar wanda ake gudanarwa a jihar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China