Mai magana da yawun majalisar dattijan kasar Aliyu Abdullahi, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, babban birnin kasar, sanarwar ta ce shugaba Buhari ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar na 1999, wanda ya tanadi cewa shugaban kasa ya mika mulki ga mataimakinsa kuma ya rubutawa majalisun dokokin kasar biyu idan ya bukaci yin hutu don duba lafiyarsa.
Abdullahi ya bayyana hakan ne domin maida martani game da zanga zangar da wasu kungiyoyin fararen hula suka yi, inda suka nemi shugaban kasar da ya yi murabus sakamkon dogon hutun jinyar da yake yi a Landan.
Ya bukaci masu zanga zangar da su daina yunkurin ruruta wutar rikici a tsarin siyasar kasar, yana mai cewa, babu abin da hakan zai haifar sai rudani marar amfani a cikin kasar.
Mai magana da yawun majalisar dattijan ya bayyana cewa, masu boren suna kokarin raba hankalin fadar shugaban kasar ne daga batutuwan tattalin arziki da tsaro, wanda a cewarsa tuni aka samo bakin zaren warwaresu.
Ya kara da cewa, majalisar dokokin kasar sun gamsu cewa babu wani gibin da aka samu a kasar. Kasancewar gwamnatin tarayya tana aikinta yadda ya kamata, ya kara da cewa mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo yana tafiyar da shugabancin kasar yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)