Yayin wani taron manema labarai da ya gudana jiya a Cairo babban birnin kasar Masar, Ahmed al-Mesmary, ya ce goyon bayan ayyukan ta'addanci na nufin Qatar na aikata laifuffukan da suka take hakkin dan Adam a Libya.
Kakakin ya ce rundunar sojin ta samu nasara, sannan ita ke rike da ikon yankuna da yawa na Libya, duk da yaki da take da kungiyoyi 4 da suka hada da IS da Al-Qaeda da ta 'Yan Uwa Musulmi da kuma wasu kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai. (Fa'iza Mustapha)