Mahalartar taron sun hada da mataimakin babban daraktan ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin Guo Weimin, da jakadan kasar Sin dake Afirka ta Kudu Lin Songtian, da wakilan kafofin watsa labarun kasar Sin dake Afirka ta Kudu, da kuma wakilan kafofin watsa labaru 15 na kasashe daban-daban dake nahiyar Afirka.
Dangane da yadda za a zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kafofin yada labaru na Sin da Afirka, mista Guo Weimin ya ce, ya kamata a karfafa fahimtar juna tsakanin kafofin watsa labarai na kasar Sin da na kasashen Afirka, tare da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin daukaka mu'amalar bangarorin biyu zuwa wani sabon matsayi. Sannan kuma, bangarorin biyu su bayyana ra'ayoyinsu yadda ya kamata a duniya bisa hadin gwiwa da mu'amalar dake tsakaninsu. (Maryam)