Asusun raya Afirka na kasar Sin da babban kamfanin kera ababen hawa na kasar Sin wato FAW sun yi hadin gwiwa sun gina wata masana'antar kera motoci a kasar Afirka ta Kudu wadda ke samar da motocin daukar kaya dubu biyar a kowace shekara. Ana kuma fatan kamfanin zai samar da guraban ayyukan yi kimanin 750 ga mazauna wurin. Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce, wannan masana'anta ba ma kawai za ta rika samar da guraban ayyukan yi da horas da fasaha a wurin ba, har ma za ta yi babban tasiri ga bunkasar sana'ar kera motoci a kasar, da raya yankin gabashin Cape Town ta yadda wata rana zai zama tamkar birnin Detroit na kasar Amurka, wanda ya yi suna ta fuskar kera motoci.