Jiya Litinin a nan birnin Beijing, kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, da bankin duniya da Jami'ar Jao Tong ta birnin Shanghai sun hada kai don shirya taron karawa juna sani game da ba da ilmi a jami'a da kimiyya karo na farko tsakanin Sin da kasashen Afirka, da nufin zurfafa hadin kai da cudanya a tsakanin kwalejin nazarin kimiyyar Sin da jami'ai da hukumomin nazarin kimiyya na kasashen Afirka, kana da karfafa karfin kasashen Afirka ta fuskar kimiyya.
Babbar kwaminishiniyar bankin duniya Liang Xiaoyan ta nuna cewa, bankinta na fatan samar da dandamali na taimakawa kasashen Afirka don samun ci gaban kimiyya da bada ilmi, ta kuma nuna imanin cewa, fasahohin da Sin ta samu wajen samun bunkasuwa za su amfanawa kasashen Afirka. (Bilkisu)