Asusun raya Afirka na kasar Sin da kamfanin TEDA na birnin Tianjin na kasar Sin, sun zuba jari a tare don gina yankin tattalin arziki da cinikayya na Suez dake kasar Masar, inda ake kokarin raya sana'o'in da suka shafi kayan wutar lantarki, da samar da tufafi, da na'urorin da ake amfani da su a kamfanonin samar da man fetur da sauransu, lamarin da ya samar da guraban ayyukan yi ga mazauna wurin kusan dubu biyu.