Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar da wasu alkaluma a yau Alhamis, wadanda ke nuna cewa, ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afirka ya bunkasa, inda jimillar cinikayya a farkon rabin bana ta karu da kashi 19 cikin kashi dari bisa na makamancin lokacin bara. A sa'i daya kuma, an samu kyautatuwar tsarin shigi da fici, da kuma aiwatar da manyan ayyuka a tsakanin bangarorin biyu yadda ya kamata.
A farkon rabin wannan shekara, tattalin arzikin Afirka ya samu farfadowa sosai. Hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka ta yi hasashen cewa, karuwar tattalin arzikin Afirka za ta kai kashi 3.2 cikin dari a shekarar 2017, karuwar kashi 1.7 cikin dari bisa ta bara.
A yayin taron manema labarai da aka shirya a yau, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, sakamakon wannan yanayin da ake ciki, Sin da Afirka na gaggauta ayyukan hadin kai dake tsakaninsu a fannonin masana'antu, aikin gona, muhimman ababen more rayuwa, sha'anin kudi da dai sauransu, lamarin da ya taimaka ga karuwar yawan cinikayya a tsakanin bangarorin biyu. (Kande Gao)