Bangaren 'yan tawayen Sudan ta kudu sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati
A jiya Lahadi ne bangaren 'yan tawayen Sudan ta kudu dake da zama a jihar Kogin Yei dake bangaren kudancin kasar suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati, a wani mataki na kawo karshen tashin hankalin da ya raba dubban mutane da matsugunansu a kasar.
Birgediya janar Hillary Edson Yakani shi ne ya sanya hannu a madadin kungiyar 'yan tawayen dake fafutukar kwatar 'yancin al'ummar Sudan bangaren adawa(SPLA IO), yayin da Manjo janar Marshal Babanen kuma ya sanya hannu a madadin gwamnati.(Ibrahim)