in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Masar da kamfanonin Sin sun cimma daidaito kan gudanar da aikin gina hanyoyin jiragen kasa
2017-07-19 13:54:08 cri
A jiya ne shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya gudanar da wani taro a birnin Alkahira, inda ya bayyana kudurin gwamnatin na hada kai da kamfanonin kasar Sin wajen gina hanyoyin jiragen kasa a wajen birnin Alkahira. Yanzu jami'an gwamnatin kasar Masar da wakilan kamfanonin Sin sun cimma daidaito a mataki na farko.

Sashen ciniki na ofishin jakadancin Sin dake kasar Masar ya bayyana cewa, kamfanin AVIC da kamfanin gina hanyoyin jiragen kasa na kasar Sin ne za su dauki gudanar da wannan aiki tare. Jami'an gwamnatin kasar Masar da wakilan kamfanonin Sin sun cimma daidaito, amma ana bukatar kara yin shawarwari don daddale yarjejeniya ta karshe.

Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasar Masar Alaa Youssef ya bayar a wannan rana ta ce, ministan harkokin sufuri na kasar Masar shi ma ya halarci taron tattaunawa game da aikin gina hanyoyin jiragen kasa tare da wakilan kamfanonin Sin. Wannan aiki dai yana daya daga cikin shirin farfado da hanyoyin jiragen kasa da ma'aikatar harkokin sufuri ta kasar Masar ta tsara. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China