in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan yankunan raya masana'antu da fasahohin zamani a Sin ya kai 146
2016-08-23 13:19:07 cri

Darektan cibiyar wutar yola ta ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Zhang Zhihong ya gabatar a jiya Litinin cewa, yawan yankunan raya masana'antu ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani na Sin ya kai 146, yawan kudin da suka samu daga wajen su a shekarar bara ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 25370.

A gun taron ba da rahoto kan sakamakon da aka samu wajen kafa yankin a birnin Tianjin, Zhang Zhihong ya bayyana cewa, bayan da aka yi shekaru 20 ana neman bunkasuwa, ya zuwa yanzu, yawan yankunan da aka kafa a kasar Sin ya kai 146, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kirkire-kirkire a kasar ta Sin.

Yawan kudin da wadannan yankuna suka samu ya karu da kashi 17.4 cikin 100 a kowace shekara tsakanin shekarar 2010 da ta 2015, wanda ribar da aka samu ya kai kudin Sin RMB sama da Yuan biliyan 1600. Yankuna 63 daga cikinsu sun samu kudaden shiga wadanda suka haura RMB Yuan biliyan 100. Ban da haka kuma, an kara gano sabbin fasahohi na yanar gizo da injin gurzawa na 3D da kuma na'urorin da aka iya sanya su kamar tufafi da sauransu a wadannan yankuna.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China