A yau Jumma'a 28 ga wata ne, aka bude taron manyan jami'an tsaron kasashen kungiyar BRICS karo na 7 a nan birnin Beijing, wanda ya kasance daya daga cikin jerin tarukan da kasar Sin ta kira yayin da take shugabancin kungiyar BRICS a bana, haka kuma taron wani muhimmin dandali ne ga kasashen kungiyar inda suke tattauna batutuwan da suka shafi hadin gwiwa ta fuskar tsaro.
A yayin taron, bangarori daban daban sun amince da cewa, za a kara kyautata tsarin taron don inganta hadin gwiwar kasashen a fannonin siyasa da tsaro. Kuma za a yi kokarin kyautata aikin daidaita lamuran duniya, da tinkarar barazara da kalubalolin da duniya ke fuskanta, ta yadda za a ciyar da dokokin kasa da kasa zuwa gaba. Bugu da kari,kasashen kungiyar za su inganta hadin kansu wajen yaki da ta'addanci, tsaron Intanet, da ma tsaron makamashi.(Kande Gao)