in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban bankin kasar Sin: An gudanar da ayyukan kudi yadda ya kamata a shekarar 2015
2016-06-28 11:18:16 cri
Jiya Litinin babban bankin kasar Sin ya kaddamar da rahoto na shekarar 2016 game da yadda aka gudanar da ayyukan kudi, inda ake ganin cewa, a shekarar 2015 kasar ta zurfafa yin kwaskwarima kan harkokin kudi a dukkan fannoni, kwarewar hukumomin kudin kasar ta karu, a hakika ayyukan kudin kasar sun gudana yadda ya kamata.
Rahoton ya nuna cewa, adadin kudade na bankunan kasar Sin a shekarar 2015 ya samu karuwa, matsayin hidimar da suka bayar kan harkokin kauyuka da sha'anin noma da manoma, da kuma kananan masana'antu shi ma ya ci gaba da karuwa. Sun kuma kara samar da rancen kudi ga wasu muhimman fannoni da wadanda suka rasa samun ci gaba, kana kuma an samu muhimmin ci gaba wajen yin kwaskwarima kan hukumomin kudi.
Kana rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2016, ya kamata a ci gaba da aiwatar da manufofin kudi cikin yakini, don inganta harkokin kudi masu amfani cikin adalci. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China