in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tallafawa shirin sarrafa amfanin gona a arewacin Ghana
2017-07-23 13:35:57 cri

Gwamnatin kasar Sin ta mika wasu kayayyakin tallafi ga wani shirin sarrafa kayan amfanin gona a arewacin kasar Ghana.

Ta hannun shirinta na habaka aikin gona a kasar wacce ke yammacin Afrika, a ranar Jumma'a gwamnatin kasar Sin ta bayar da gudummowar wasu injunan sarrafa hatsi guda 13, da wasu injunan biyu na sarrafa waken soya ga hukumar dake kula da ayyukan cigaban yankin arewacin Savannah na kasar Ghana.

Da take gabatar da tallafin kayayyakin da zummar taimakawa fannin sarrafa kayan amfanin gona a arewacin kasar, jakadar kasar Sin a Ghana, Sun Baohong, ta nanata cewa kasarta ta samu nasarori masu yawa a fannin aikin gona ne saboda muhimmancin da gwamnatin Sin take bayarwa a fannin, sakamakon amfani da manyan fasahohin zamani da kuma aiwatar da managartan shirye-shirye.

Kana ta yabawa aniyar gwamnatin Ghana sakamakon kaddamar da shirin "gunduma daya masana'anta daya" da "kauye daya madatsar ruwa daya" da "shuke-shuke don samar da abinci da ayyukan yi", inda ta bayyana cewa wannan ya nuna a fili yadda gwamnatin kasar ta himmatu wajen bunkasa fannin aikin gona.

Ta kara da cewa, sama da shekara guda, kasashen Sin da Ghana sun kulla yarjeniyoyi a fannonin aikin gona masu yawa wadanda za su amfanawa bangarorin biyu. Kasar Sin tana samar da damammaki na bada horo ga kasar Ghana inda take gayyatar kwararru a fannin aikin gona don ba su horo.

Da yake amsar kayayyakin tallafin, minista na musamman mai tallafawa ayyukan cigaban kasar Ghana Mavis Hawa Koomson, ya bayyana cewa wadannan tallafin kayayyaki sun zo ne a lokacin da ya dace, kasancewa za su tallafawa shirin da gwamnatin kasar Ghanan ke dab da kaddamarwa.

Ministan na Ghana ya ce, ziyarar da mataimakin shugaban kasar Ghanan Mahmud Bawumia ya kai kasar Sin a kwanan nan, da kuma halartar bikin rantsar da shugaban kasar Ghana Addo Dankwa Akufo-Addo da wani kusa a gwamnatin kasar Sin ya yi, wasu alamu ne dake nuna irin yadda ake samun kyakkyawar dangantakar moriyar juna tsakanin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China