A jiya Lahadi ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Zambia ya fitar da wata sanarwa game da batun Sinawa 31 da aka tsare a lardin Copperbelt na kasar, inda ya bukaci bangaren Zambia da ya saki Sinawan ba tare da bata lokaci ba. Kawo yanzu dai, ofishin jakadancin ya aika da ma'aikatansa don tattaunawa da mahukuntan na Zambia kan wannan batun, tare da ziyartar Sinawan da aka tsare.
A kwanan baya ne, hukumar kula da kaurar jama'a ta Zambia ta tsare Sinawa 31 da ke lardin Copperbelt bisa hujjar wai suna sayen danyun ma'addinin tagulla ba bisa doka ba.(Kande Gao)