An dai kame Sinawan ne dake aiki da wani kamfanin sarrafa tagulla, bisa zargin sayen danyar tagulla daga wasu 'yan kasar ba bisa ka'ida ba. To sai da mahukuntan lardin sun gaza gabatar da cikakkun shaidu game da hakan.
Sakin mutanen dai ya biyo bayan tattaunawa tsakanin jami'an ofishin jakadancin Sin dake Zambia da mahukuntan lardin na Copperbelt. (Saminu)