Madam Hua ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau a nan birnin Beijing, inda ta jaddada cewa, har kullum gwamnatin Sin na bukatar kamfanonin ta da Sinawa dake kasashen ketare za su bi dokokin wurin da suke, kuma ba ta kare duk wani aiki da ya saba wa dokoki, amma kuma tana adawa da dukkanin wasu matakai na matsawa Sinawa dake ketare. (Bilkisu)