Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane bakwai ne suka gamu da ajalinsu kana wasu 15 kuma suka jikkata sakamakon wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kaddamar jiya da dare a sansanonin 'yan gudun hijira dake kusa da garin Maiduguri a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wani ganau da ya bukaci a sakaye sunansu ya bayyana cewa, wasu mata 'yan kunar bakin wake ne suka kaddamar da hare-haren a sansanin 'yan gudun hijira na Dalori mai nisan kilomita 4 daga Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, lokacin da galibin 'yan gudun hijirar ke barci.
Sai dai har yanzu jami'an tsaro a jihar Borno ba su tabbatar da aukuwar hare-haren ba. Amma mazauna yankin na cewa, da alamun kungiyar Boko Haram ce ta kai wadannan hare-hare. (Ibrahim)