in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Duk da ana tsaka da fuskantar matsalar tsaro, Gwamnatin Nijeriya ta ce ba za a rufe Jami'ar Maiduguri ba
2017-07-29 12:36:15 cri

Gwamnatin Nijeriya ta ce babu wani shiri na bada umarnin rufe Jami'ar Maiduguri dake birnin mafi girma a yankin arewa maso gabashin kasar, duk kuwa da karuwar hare-hare kan Jami'ar da Kungiyar Boko Haram ke kai wa.

Ministan ilimi na kasar Mallam Adamu Adamu, ya shaidawa manema labarai cewa, duk da kisan da aka yi wa wasu ma'aikatan jami'ar da kuma yanayin da tsaro ke ciki a yankin, Gwamnati ba za ta so harkokin karatu su gamu da cikas ba.

Maimakon haka, a shirye Gwamnati ta ke ta bada dukkan goyon bayan da ake bukata wajen tabbatar da tsaro a yankin.

A ranar Talata da ta gabata ne jami'an Jami'ar 5 suka mutu sanadiyyar kwantar bauna da mayakan Boko Haram suka yi musu a wani gari dake kusa da birnin Maiduguri.

Harin shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren da ake kai wa jami'ar da jami'anta.

A cewar shugaban Jami'ar, Ibrahim Njodi, wadanda suka mutu yayin harin sun hada da kwarraru masu nazarin karkashin kasa 2 da takwarorinsu na harkokin fasaha 2 da kuma direba.

Har kawo yanzu akwai wasu jami'ai 4 da suka bata sama ko kasa, wadanda suka hada da malamai 2 da wani masani kan harkokin fasaha da kuma direba.

An farwa mutanen ne yayin wani aikin hadin gwiwa da suke da kamfanin mai na kasar, wanda aka fara a farkon makon nan da nufin binciken mai a yankin tafkin Chadi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China