in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya yayi alkawarin samar da miliyoyin ayyukan yi cikin shekaru 5
2017-07-24 13:04:45 cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta wanda yake neman a sake zabarsa a shugabancin kasar a karo na 2, yayi alkawarin cewa zai samar da guraben ayyukan yi kimanin miliyan 6.5 masu matukar inganci, musamman ga matasan kasar a cikin wa'adin shekaru 5 masu zuwa.

Kenyatta, wanda ya yi hira ta kai tsaye ta shafin sada zumunta na facebook, inda ya amsa tambayoyi daga al'ummar kasar Kenyan game da tanade tanaden da gwamnatinsa ta yi, yace daga cikin manufofinsa shine ya kuduri aniyar samar da ayyukan yi masu yawa kuma zai rage tsadar farashi a kasar daga inda aka tsaya cikin shekaru 4 da suka gabata ta yadda al'ummar kasar Kenyan zasu ci gajiya.

Ya kara da cewa kudurorin da yake da su zasu tabbatar da sake fasalin cigaban kasar da gwamnatinsa ta faro su cikin shekaru hudun da suka gabata, a cikin shekaru 5 masu zuwa zai samar da ingantattun ayyukan yi miliyan 6 da rabi ga al'ummar kasar musamman matasa, Kenyatta ya bayyana hakan ne ga masu bibiyarsa a shafin facebook su kimanin miliyan 3.

Tattaunawar ta kai tsaye an gudanar da ita ne ta tsawon mintoci 45, Kenyatta yana neman karin wa'adin mulki ne na shekaru 5, ya tattauna batutuwa masu yawa a lokacin hirar tasa ciki har da batun yaki da cin hanci, tsaro da kuma zaben kasar dake tafe a ranar 8 ga watan Augasta.

Yace dukkan 'yan kasar nada rawar da zasu taka wajen yaki da rashawa, kuma a cewarsa, a matsayinsa na shugaban kasar zai sadaukar da kansa wajen yaki da rashawa.

Kenyatta yace a shirye yake ya yaki rashawa kuma zai baiwa bangaren shari'a dama ya gudanar da aikinsa na tabbatar da adalci da hukunta dukkan wanda aka samu da hannu wajen aikata laifuka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China