Da yake tabbatar da hakan yayin wani taro da manyan hafsoshin tsaron kasar, da ma sauran mahukunta a birnin El Fasher, fadar mulkin jihar Arewacin Darfur, mataimakin shugaban kasar Sudan Hasabo Mohamed Abdul-Rahman, ya ce gwamnati na fatan ganin an raba daukacin fararen hular yankin da bindigogi marasa rajista, da sauran ababen hawa marasa lasisi. (Saminu Hassan)