in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan zata ci gaba da hadin gwiwa da Amurka duk da takunkumin da aka aza mata
2017-07-14 09:25:42 cri
A ranar Alhamis gwamnatin Sudan ta sanar da cewa zata cigaba da yin hadin gwiwa da Amurka duk da dakatarwar da aka yiwa kwamitin da aka kafa wanda zai duba hanyoyin cimma matsaya don cire takunkumin da Amurkar ta kakabawa Sudan din.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, ya sanar da cewa ya jingine kwamitin sasantawar da gwamnatin Amurka har zuwa ranar 12 ga watan Oktoban wannan shekara.

Wannan mataki ya biyo bayan matakin da Amurkar ta dauka ne na dakatar da lokacin da za'a duba yiwuwar cire takunkumin na dindindin kan kasar ta Sudan, sai nan da watanni uku masu zuwa.

Ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Ghandour, ya bayyana a taron 'yan jaridu cewa, matakin dakatar da kwamitin sasanton da aka yi, ba yana nufin an katse dangantakar dake tsakanin Khartoum da Washington ba ne.

Ghandour ya bukaci Amurka da ta cika alkawarinta na cire takunkumin data kakabawa Sudan din nan da watan na Oktoba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China