in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya dakatar da aikin kwamitin tattaunawa da Amurka
2017-07-13 15:16:31 cri
Shugaba Omar al-Bashir na Sudan, ya dakatar da aikin kwamitin kasar sa wanda ke tattaunawa da tsagin Amurka, game da burin dage takunkumin da Amurkan ta kakabawa kasar sa.

A jiya ne dai shugaba al-Bashir ya ayyana dakatar da aikin kwamitin ya zuwa ranar 12 ga watan Oktoba mai zuwa, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na SUNA ya rawaito.

Da yake karin haske game da hakan a birnin Khartum, ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour, ya ce kasar sa ta dauki wannan mataki ne bisa jin cewa Amurka, ta dage batun janyewa Sudan din takunkumi, ya zuwa karin wasu watanni 3 masu zuwa. Matakin da a cewar sa sam bai dace da adalci ba.

Kafin hakan dai mahukuntan Amurka sun fidda sanarwa ta dakatar da duk wasu matakai, wadanda za su kai ga dage takunkumin da ta sanyawa Sudan din ya zuwa karin watanni 3, ko da yake dai ba ta gabatar da wasu dalilai na zahiri da suka haifar da hakan ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China