Yayin da take holinsu a jiya, rundunar 'yan sandan ta ce ta yi nasarar cafke mutanen ne bayan ta gudanar da binciken kwakwaf game da inda sansanoninsu suke.
Kakakin rundunar 'yan sandan Mashood Jimoh, ya ce an kuma kubutar da wasu mutane da aka sace yayin samamen.
Wadanda ake zargin da suka kunshi 'ya'yan kungiyoyi mabambamta, sun amsa laifinsu, kuma wasu daga cikin mutanen da aka kubutar sun gane wadanda suka sace su.
Mutanen da aka kama na gudanar da ayyukan nasu ne a kan babban titin Kaduna zuwa Abuja.
Kakakin 'yan sandan ya ce za a gurfanar da mutanen da ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
A ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata ne, rundunar 'yan sanda Najeriya ta fara aikin sintiri da aka yi wa lakabi da "Operation Absolute Sanity" a kan babbar hanyar da ta hada birnin Kaduna dake yankin arewa maso yammacin kasar ta kuma birnin Abuja.
Cikin kasa da mako guda bayan 'yan sanda sun fara aiki a yankin, sun yi nasarar damke wadanda ake zargi da satar mutane guda 31, sannan sun lalata sansanoninsu. (Fa'iza Mustapha)