in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD game da harkokin Syria zai halarci tattaunawa a Astana
2017-05-03 10:53:26 cri
Wakilin musamman na MDD game da batun kasar Syria Staffan de Mistura, zai halarci wani muhimmin taro game da sha'anin rikicin Syria a Astana, babban birnin kasar Kazakhstan, a ranakun 3 zuwa 4 ga wannan wata na Mayu.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Talata, yace domin daukar matakan gaggawa na shawo kan rikicin da ya daidaita kasar ta Syria, ya zama tilas a hanzarta daukar kwararan matakan shawo kan matsalar da kuma sake gina kasar, ya kara da cewa mista Staffan zai halarci taron a matsayin mai sa ido don amsa gayyatar da gwamnatin Kazakh ta yi masa.

A yayin da yake birnin na Astana, wakilin na musamman zai taimakawa duk wani yunkuri na masu shiga tsakani don tabbatar da shirin tsakaita bude wuta da kuma hana daukar dukkan matakai na soji. Jami'in zai kuma halarci taron ne tare da rakiyar tawagar kwararru na MDD wadanda sun sha halartar taron na birnin Astana.

De Mistura, zai kuma yi amfani da wannan dama wajen shiga tattaunawar siyasa don tuntubar masu shiga tsakani game da shirin tsakaita bude wuta, kuma wannan zai kasance tamkar daura danba ne game da taron da ake saran gudanarwa a nan gaba a birnin Geneva game da warware rikicin na Syria. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China