in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun juyin juya hali na Iran sun kai harin makami mai linzami kan 'yan ta'adda a Deir ez-Zor na Syria
2017-06-19 10:13:08 cri
Dakarun juyin juya hali na Iran (IRGC) sun ba da sanarwa a ranar Lahadi cewa, sashen kula da sararin samaniya na IRGC ya kaddamar da harin makamai masu linzami kan maboyar 'yan ta'adda dake yankin Deir ez-Zor na kasar Syria.

Jami'in hulda da jama'a na IRGC ya bayyana cewa, makasudin kaddamar da harin makamai masu linzamin shi ne, domin murkushe 'yan ta'adda na "Takfiri" saboda harin tagwayen bomai bomai da suka kaddamar a kwanan nan a Tehran, babban birnin kasar Iran.

Dakarun na IRGC sun harba makamai masu linzami masu matsakaici gudu ne daga lardunan Kermanshah da Kurdistan dake yammacin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, harin ya yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda masu yawa, tare kuma da lalata musu makamai da alburusai masu yawan gaske.

Dama dai IRGC, ta sha alwashi mayar da martani dangane da harin da 'yan ta'addan suka kaddamar a Jamhuriyar Musulunci ta Iran. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China