An yi nasarar ceto wasu mutane 15, ciki har da wani yaro dan shekara 11.
Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta yankin kudu maso yammacin Nijeriya NEMA Ibrahim Farinloye, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kafafun yaron mai shakara 11 sun riga sun guntule a lokacin da aka ciro shi daga burbushin ginin.
An ceto yaron ne da sanyin safiyar jiya Laraba, sama da sa'o'i 12 bayan ginin ya rushe.
Tawagar masu ceton, da ta kunshi jami'an NEMA da na hukumomin tsaron jihar da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar LASEMA sun kammala aiki a wajen, bayan sun kai matakin karshe na gini da misalin karfe 1:30 na rana agogon Nijeriya.
Masu ceto sun shafe tsawon daren ranar Talata suna ceton mutane da ginin ya rufta da su. Kuma an kai manya-manyan kayayyakin aiki domin gudanar da bincike cikin burbushin ginin. (Fa'iza Mustapha)