Ibrahim Idris ya bayyana haka ne jiya a Abuja, fadar mulkin kasar, inda ya ce abun takaici ne, yadda masu satar mutane suka fi masu kishin kasa samun 'yanci a Nijeriya.
Ya ce har yanzu, ba a ga inda aka gurfanar tare da yanke hukuncin zaman gidan yari ga wadanda ake zargi da satar mutane ba.
Babban Sufeton wanda ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga shugabannin rundunonin 'yan sandan jihohin kasar, ya ce tsaurara hukunci kan masu satar mutane zai sa su kauracewa mummunar dabi'ar.
Matsalar satar Mutane ta zama ruwan dare a Nijeriya, inda har ya kai matakin da za a ce da wuya rana ta wuce, ba tare da samun labarin satar wani ba a sassan kasar. (Fa'iza Mustapha)