in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu tana neman karfafa hulda da kasar Sin
2017-06-04 12:31:14 cri
Sudan ta kudu tana neman karfafa hulda da kasar Sin yayin da ta nuna gamsuwa da tsarin nan na moriyar juna na kasar Sin, wani babban jami'in kasar ne ya tabbatar da hakan.

Ministan kudi da tsara tattalin arziki na Sudan ta kudun Stephen Dhieu Dau, ya ce kasar Sin ta ba da gagarumar gudunmowa wajen dorewar kasar Sudan ta kudun tun baya da kasar ta tsunduma cikin yakin basasa a watan Disambar shekarar 2013, ya kuma kara da cewa gwamnatin Sudan ta kudun tana kokarin karfafa dangantaka da kasar Sin domin amfanin kasashen biyu.

Dau ya ce, gwamnati da al'ummar Sudan ta kudun su na kokarin kara lalibo wasu muhimman hanyoyi na kara yin cudanya da kasar Sin, saboda sun yi amanna da manufofin kasar Sin game da hulda da kasashen Afrika da kuma Sudan ta kudun cewar an gina su ne bisa mutunta juna da cigaban rayuwar bil adama.

Ministan ya bayyana hakan ne a babban birnin kasar Juba a lokacin bikin mika wasu nau'rori na yaki da cutar malariya a duk fadin kasar wanda gwamnatin Sin ta bada gudumowarsu ga Sudan ta kudun.

Kasar Sudan ta kudu ta dogara ne kacokan kan albarkatun man fetur, inda take samun kashi 98 cikin 100 na kudaden kasafin kudinta daga man fetur, sai dai aikin hako danyen man kasar ya gamu da cikas sakamakon barkewar yakin basasa a kasar, lamarin da ya tilasta rufewa mafi yawan rijiyoyin man kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China