Gwamnan Babban Bankin Farfesa Patrick Njoroge, ya shaidawa wani taron manema labarai a birnin Nairobi cewa, raguwar farashin kayayyakin abinci ne zai haifar da saukar matakin daga kashi 9.2 da yake kai a yanzu.
Farfesa Njoroge ya ce a yanzu, Kenya ta daura damarar rage matakin hauhawar farashin kayayyaki zuwa kasa da kashi 7.5, inda ya ce abu ne mai wuya a yi hasashe takamaimai, saboda za su dogara ne akan farashin kayayyakin abinci da aka fi bukata.
Bankin ya sanya matakin da yake son cimmawa tsakanin kashi 2.5 da 7.5.
Gwamnan ya kara da cewa, matakin hauhawar farashin kayayyaki ya sauka a baya-bayan nan saboda tasirin ruwan sama kan harkokin samar da abinci da kuma matakan Gwamnati na takaita tsadar abinci.
Ya kara da cewa, sauye-sauyen harkokin kudi ba ya tasiri a kan farashin kayayyakin gona, kamar sauran kayayyaki.
A ranar Litinin da ta gabata ne kwamitin kula da hada-hadar kudi na Babban Bankin kasar ya bar matakin hauhawar farashi a kan kashi 10 cikin dari ta yadda zai yi daidai da hasashen da aka yi. (Fa'iza Mustapha)