in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNSC ya amince da kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi saboda gwajin makaman nukiliya da ta gudanar sau 2 a watan Yuli
2017-08-06 13:51:05 cri
Kwamitin tsaron MDD a ranar Asabar ya yi amincewa ta bai daya game da kudurin da Amurka ta gabatar na neman kakabawa Koriya ta Arewa DPRK takunkumi, inda kwamitin ya amince da rage kaso uku na kudaden kimanin dalar Amurka biliyan 3 wanda DPRK take samu a duk shekara na kudaden shigarta a sakamakon gwajin makaman nukiliya da ta yi har sau biyu a watan Yuli.

Matakin zai haramtawa DRPK samun damar fitar da ma'adananta na kwal, karfe, tama da karafa, darma da abincin ruwa. Kudurin zai kuma haramtawa kasashen duniya kara yawan ma'aikatan kwadagon na DPRK dake ayyuka a kasashen waje da kuma haramta sabbin zuba hannayen jari a kasar.

Kuduri mai lamba 2371, ya samu amincewar dukkan wakilan mambobin kwamitin tsaron MDDr a ranar Asabar, wanda ya karfafa matakan aza takunkumin kan DPRK ne don mayar da martani kan gwajin makaman nukilyar da ta gudanar a ranar 3 da kuma 28 ga watan Yuli.

Daukar wannan mataki, ta bayyana a fili cewa, kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da saba ka'idojin da DPRK ke yi kuma ana bukatar kasar da ta dakatar da shirinta na makaman nukiliyar baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China