in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Rwanda: Layin Mombasa-Nairobi na da muhimmanci matuka
2017-06-10 12:24:06 cri
Ministan kasar Ruwanda mai kula da harkokin kudi da tsarin tattalin arziki, Claver Gatete ya bayyana layin dogon da wani kamfanin kasar Sin ya gina, wanda ya hada biranen Mombasa da Nairobi a matsayin mai ma'ana sosai ga yunkurin dinkewar kasashen dake gabashin Afirka waje guda.

Claver Gatete wanda ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis a Kigali, fadar mulkin kasar, ya ce layin dogon abu ne da jama'ar kasashen Afirka ke alfahari da shi, wanda zai taimaka wajen rage kudin da ake kashewa domin jigilar kayayyaki da fitar da su zuwa kasashen waje, sannan zai sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin yankin gabashin Afirka.

Yanzu haka kasashe da suka hada da Ruwanda sun dauki niyyar shimfida wasu sabbin layukan dogo domin hada dukkan kasashen dake yankin.

Ban da haka kuma, jami'in ya kara da cewa, Rwanda na da kyakkyawar hulda da kasar Sin, kuma za ta yi kokarin hada gwiwa da kasar Sin a fannoni daban daban, don mai da dangantakar dake tsakaninsu matsayin wani abin koyi ga sauran kasashen duniya.

An kaddamar da layin dogon da ya hada Mombasa da Nairobi ne a ranar 31 ga watan Mayun da ya gabata, wanda tsawonsa ya kai kilomita kimanin 480, kuma ta wannan layi aka fara aikin gina wata yanar gizo ta layukan dogo a gabashin Afirka.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China