Wata sanarwa da masu shirya bikin suka fitar a jiya Juma'a, ta ce za a gudanar da bikin na dare ne a ranar 24 ga watan nan a cibiyar baje koli ta Kigali, wanda ake kira da Kigali Camp, kuma wadanda za su karbi lambar yabon sun hada da fitattun masu shirya fina-finai da jarumai maza da mata a matakai 28.
Bikin na zaman wani gagarumin taro na masana'antar shirya fina-finai, kuma babban taron da zai samu halartar masu ruwa da tsaki kan harkar shirya fina-finan a nahiyar Afrika.
Cibiyar bada lambar yabo ta Afrika wato AMAA wadda aka kafa a shekarar 2005 da nufin ciyar da harkokin shirya fina-finai gaba a Afrika ce ta shirya bikin.
Wandanda aka zaba da a cikinsu za su samu lambar yabo su 155 ne ake sa ran za su hallara a Kigali domin bikin na bana.
Fitattun jaruman wasa 'yan Nijeriya kamar Ramsey Nouah da masu bada umarnin da shirya Fina-finai da suka hada da Lydia Forson 'yar kasar Ghana da Emem Isongo, Nkem Owoh, Rita Dominic na Nijeriya ne ake sa ran suma za su halarci bikin. (Fa'iza Mustapha)