in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya mayar da martani ga kalaman da Donald Trump ya yi game da "yarjejeniyar Paris"
2016-11-01 19:02:26 cri
A yau Talata ne, Mr. Xie Zhenhua, wakilin kasar Sin kan batun tinkarar sauyin yanayin duniya ya ce, yana da imani cewa, idan shi shugaba ne mai hankali, ya kamata ya san cewa, dukkan manufofi da matakan da zai dauka su dace da ka'idodin da ake bi a duk duniya."

Mr. Xie ya fadi haka ne a yayin da yake mayar da martani ga kalaman nuna adawa da "yarjejeniyar Paris" da Mr. Donald Trump, dan takarar shugabancin kasar Amurka ya yi.

A kwanan baya ne, Donald Trump ya bayyana cewa zai yi watsi da "yarjejeniyar Paris" da aka kulla a shekarar 2015, har ma ya nemi kasar Amurka da ta janye daga wannan yarjejeniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China