in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe sama da 165 sun nuna niyyar daddale yarjejeniyar Paris a yau
2016-04-22 10:01:15 cri
A jiya Alhamis 21 ga wata, kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, kasashe sama da 165 sun bayyana niyyarsu cewa, za su rattaba hannu kan yarjejeniyar Paris a yau Jumma'a 22 ga wata.

A jiya ne Stephane Dujarric ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, kasashe sama da 165 sun bayyana cewa, za su daddale yarjejeniyar Paris a gun bikin sa hannu bisa a matsayin koli da za a shirya a hedkwatar MDD a ranar 22 ga wata, inda shugabanni da kusoshin gwamnatocin kasa da kasa kimanin 60 za su halarci bikin.

Bayan haka, Stephane Dujarric ya ce, daddale yarjejeniyar Paris, matakin farko ne na tabbatar da gudanar da ita tun da wuri. Bayan haka, dole ne kasa da kasa su sami izini a kasashensu. Kasashe 13 sun riga sun bayyana cewa, za su mika izininsu ga babban sakataren MDD Ban Ki-moon a yau.

Bisa jadawalin da MDD ta gabatar, an ce, a yau Ban Ki-moon zai jagoranci bikin sa hannu, yayin da wakilan kasa da kasa za su sa hannu a kan yarjejeniyar Paris bi da bi, daga bisani za su gabatar da jawabai a kai.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China