in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a samar da daidaito da kara aminta da juna wajen kare teku a duniya
2017-06-08 10:00:08 cri
Jami'in kasar Sin dake halartar babban taron MDD kan kare teku, ya yi kira da a inganta samar da daidaito da aminta da juna wajen kare teku a duniya.

Mataimakin Daraktan hukumar kula da sha'anin teku na kasar Sin Lin Shanqing, wanda ya bayyana haka yayin zaman taron a jiya Laraba, ya ce akwai bukatar al'ummomin kasashen waje su inganta hadin kai wajen kare tekuna.

Lin Shanqing, ya ce la'akari da matakan da ta bi wajen samun ci gaba, a shirye kasar Sin take ta taka muhimmiyar rawa wajen kulla ingantacciyya hadin gwiwa mai karfi da sauran kasashe da hukumomin ta yadda za a mori juna wajen kare gurbatar teku.

Taron na MDD kan kare teku na gudana ne a hedkwatar majalisar dake birnin New York, daga 5 zuwa 9 ga watan Yuni, inda ranar kare Teku ta duniya wato 8 ga watan Yuni za ta fada cikin ranakun da ake taron.

Mataimakin Daraktan ya bayyanawa taron cewa, kasar Sin ta dauki matakan kare muhallin halittun cikin teku.

Ya ce an shata wasu yankunan halittun teku, inda karkashinsa, aka kebe wasu yankunan masu matukar muhimmanci da ake sa ido sosai kan abubuwa dake gudana a wuraren. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China